Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A yayin ganawar, Jagora (H) ya jaddada muhimmancin fahimtar ma'anar jiran Imam Mahdi (AS). Inda yace, aiki ne. “In dai Shi'ar Imam (AS) kake, to hanyarsa za ka bi. Don in ya zo, zai sami dakarunsa ne a shirye. Ba zai fara daga ba wanda zai amsa masa ba ne.”
Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa, in Imam Mahdi (AS) ya bayyana, an ce zai zama yana da hawa-hawa na mabiya, akwai 313, a gaba, an ce akwai ko 700 ne, sannan a gaba akwai guda kaza. Haka nan hawa-hawa. Yace: "Kuma abin ban-mamaki, an ce a cikin 313 din nan (na mabiyansa), akwai mata da yawan gaske. To su wadannan mutanen za a jira ne sai ya zo za a haife su?”
Yace, za su zama dama akwai su ne. Kuma zai zama dama suna aikinsa ne. Shi ne jira din. Don haka yace, “wannan aikin zaman jiran ne ya hau kanmu yanzu.”
Da yake bayani dangane da aikin Harisanci, Jagora (H) ya bayyana aikin Harisanci a matsayin ƙari akan ayyukan Harka. “Aikin 'yan uwa duk iri daya ne, amma sai aka ce to ga wani kuma ƙari na wadannan mutanen da ake ce musu Harisawa, wanda su an sa su gadin abubuwa. An sa su su tsaya da wadansu ayyuka.”
Yace: “Alhamdulillahi, an tsaya da wasu ayyuka wanda ake yi a Harka da ma a wajen Harka, da raimaka ma al'umma da sauransu. Wanda kuma na san kwafanmu yana da wahala.”
Ya cigaba da cewa, wasu suna kokarin su kwafe mu, amma ba zai yiwu ba, saboda inda manufar mu yake ya bambanta. “Su ta yiwu su yi domin ko a yaba musu. To amma in kana yin abu don Allah, to ya bambanta.”
Jagora (H) ya jaddada cewa: “Kullum na kan gaya ma 'yan uwa, a yi saboda Allah. Kullum na kan ce, yi saboda Allah, yi saboda Allah, yi saboda Allah.”
Yace, aiki tare yana da wahala, domin abin da zai fi bakanta maka rai shi ne, wadanda za su baka wahala, ba wasu na waje ba ne, wadanda kake tare da su ne. “Kai wannan abu da ban al'ajabi. Wanda kuke tare su za su yi ta abubuwa, suna cewa, ka ga wannan, wai shi yana nuna ya fi kowa, wuuu, in ba a kawar da wannan ba, wallahi Harisancin ma ba zai yiwu ba, kaza-kaza. Ko a dinga, ai wane yana kaza ne. Tsegungunma irin wannan. (Don haka), in dai kana yin abin ka saboda Allah ne, to kyale ka yi ta ta yin abinka saboda Allah din kawai. Amma in za ka damu da cewa an dame ka, to sai ka fasa.”
Yace, in ka fasa kana yi saboda mutane kenan. “In kana abinka saboda Allah, duk abinda za su yi ta fada, su yi ta fada. Kai kuma ka tsaya kyam ka yi abinka saboda Allah.”
Jagora (H) ya bayyana yi domin Allah a matsayin babban abinda zai zama ma mutum Jagora. “In haka nan kake yi, to ba ruwanka. Suka ne, yabo ne, duk daya ne, kai dai ka yi saboda Allah, kuma ladanka na wajen Allah. Insha Allahul Azeem.”
Jagora (H) ya kuma yi gyara ga shekarun da Hurras Central suka ayyana na mata masu ritaya, daga 45 zuwa 55. Inda yace: "Muka ce, lallai abinda ya kamata, in dai Harisanci ne, ya kamata ya zama akwai wani gwargwado lokacin da za ka yi... Shekaru 55 ya yi daidai. To amma ban sani ba, idan mata suka ce ya yi yawa, sai a rage musu. In su suka ce, gaskiya ita mace dai in ta kai 45 ya kamata a sauwake mata, ka ga sai a sauwake. In ba haka ba, ita ma 55 din ya kamata.”
Ya kuma bayyana yadda a shekarun baya akan yi Faretin Harisawa a daidai wannan lokaci. Yace amma yanzu zuruf basu ba da damar hakan ba. Watarana za a yi. Yace, “Shi yasa aka gaiyato kwamandodin eriyoyi daban-daban, aka zo aka tattauna. Na san an yi shawarwari daban-daban, ni nawa karkarewa ne. Amma dai maganar nan da nake yi, shi ne muhimmi, cewa lallai kyakkyawar Iklasi shi ne muhimmin abu. Ka yi abu saboda Allah. Insha Allahul Azeem.”
Jagora ya yi fatan ganin cigaba daga bangaren na Harisawa a nan gaba. Sannan ya karkare da addu'ar: “Allah Ta'ala Ya bamu dakewa, Ya tabbatar da duga-duginmu, Ya hada kawukanmu. Ya sa muna cikin dakarun da za su taimaka ma Imam (AJ).”
Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
17/Sha’aban/1447
05/02/2026
Your Comment